
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ya gama da babban dan Adawa, Atiku Abubakar saboda har wanda yayi masa mataimaki a zaben shekarar 2023, Ifeanyi Okowa ya koma jam’iyyar su ta APC.
Ya bayyana cewa ko gamayyar da suke hadawa a yanzu ta watse.
Inda ya karkare da cewa, Ya sake yin nasara akan Atiku Abubakar.
A jiyane dai Ifeanyi Okowa ya koma jam’iyyar APC daga PDP