Friday, December 5
Shadow

Na Gano cewa: Yawanci mazan Kano basa iya ciyar da matansu, sannan ana yiwa yara mata auren wuri>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce dole ne a gyara zamantakewar aure a tsakanin ma’auarata a jihar Kano kasancewar matsalar ce ta fi damun al’ummar jihar Kano.

Sarkin na Kano ya ce ƙararrakin ciyarwa su ne kaso mafi yawa na shari’o’in aure da aka fi samu cikin kotunan jihar a shekarun baya-bayan nan.

Wannan wani ɓangare ne na kundin binciken digiri na uku na dokar shari’ar Musulunci da Khalifa Muhammadu Sanusi ya rubuta bayan kammala karatunsa a Jami’ar London.

Auren kananan yara

Sarki Muhammadu Sanusi ya ce wani abun da ya fahimta shi ne idan ana son a kawo ƙarshen yi wa ƙananan yara aure dole ne sai gwamnati ta taka muhimmiyar rawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Auren da Rahama Sadau ta yi ta kyauta, Ki daure ki zauna a gidan mijinki, ki masa biyayya>>Inji Malam

“Har yanzu ina kan ra’ayin lallai ya kamata a bar yarinya sai ta girma a yi mata aure. Kuma a cikin bincike abubuwa da dama sun bayyana. Misali a ƙasarmu ma ba ma rubuta ranar haihuwa. Saboda haka ko an yi dokar, idan mahaifin yarinya ya ce shekarar ƴarsa 18, wane ne kai ka ce ba haka ba ne ba.”

“Saboda haka kafin a magance matsalar auren ƙananan yara dole ne sai an haɗa da wa’azi da gina makarantu da ajiye malamai da tallafawa talakawa.”

Sako ga matasa

Sarki Sanusi ja hankalin matasa game da matuƙar muhimmancin tattalin lokaci a rayuwarsu ta hanyar neman ilmi da shiga al’amura masu ma’ana tun suna kan ganiyarsu maimakon shafe tsawon lokaci a shafukan sada zumunta.

Karanta Wannan  Kalli An Gano Mawakin Najeriya Davido yayi amfani da hoton karya dan ya burge masoyansa

“Matasa suna ɓata lokacinsu kuma idan aka duba za ka ga matasan Kudu ba haka suke yi ba. Matasan Yarabawa da Igbo suna can suna karatu suna ilimi. Idan namu ba su yi hankali ba to za su zama bayin wadancan tunda mu za mu tafi ne. Saboda haka cigaban ƙasarmu ya dogara ne kan ilimin yaranmu maza da mata…” A kalaman Sarki Muhammadu Sanusi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *