
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya ji dadin dawowa Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen Japan da Brazil.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace daya daga cikin aikin da ‘yan Najeriya suka bashi a shekarar 2023 shine na kulla hadaka da kasashen Duniya dan kawo ci gaba.
Shugaban yace a ziyarar da ya kai kasashen Brazil da Japan Najeriya ta kulla yarjejeniya da kasashen a fannonin kudi, sufuri, kimiyya da fasaha da sauransu.