Friday, December 5
Shadow

Na umurci jami’an tsaro su gaggauta dawo da ƴan matan Kebbi – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana takaicin sace ƴan matan da aka yi a Kebbi, da kuma alhinin mutuwar Birgadiya Janar Musa Uba da gwarazan sojojin da suka mutu a jihar Borno.

A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce ya shiga matuƙar damuwa kan mutuwar sojojin ƙasar da ke bakin aiki.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma saƙon jaje da iyayen ɗaliban da aka sace, inda ya ce yana ci gaba da yi musu addua.

” Ina cikin damuwa sosai kan yadda ƴan bindiga suka katse wa ƴan matan nan karatunsu, na umurci jam’ian tsaro su yi gaggawar dawo da ƴan matan gida” ” Ina sane da ƙaruwar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar, kuma na bai wa jami’an tsaro umurnin daƙile matsalolin cikin gaggawa”. a cewar shugaban.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai mayar da Gwamna Fubara kan mukaminsa na Gwamnan jihar Rivers, ji sharudan ban mamaki da aka gindaya masa

Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar da su taimaka wa jam’ian tsaro wajen basu haɗin kai da kuma bayanai masu muhimmanci, inda ya sha alwashin hukunta masu yi wa tsaron ƙasar barazana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *