Friday, December 5
Shadow

Na yi amanna dari bisa dari Tinubu ne zai sake cin zabe a 2027, saboda babu wani dan takara me karfi da zai iya kayar dashi daga ADC>>Inji Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, yayi imani dari bisa dari Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ne zai sake cin zabe a shekarar 2027.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Shehu Sani yace har yanzu babu wani dan takara da ya gani me karfi da zai iya mayar da shugaban kasar a Yanzu.

Yace yawanci yanzu ana kuka da Tinubu ne saboda cire tallafin man fetur amma an baiwa gwamnoni suna aiki ne saidai mutane na yabon Gwamnonin tare da mantawa cewa, shugaban kasa ne ya basu kudin.

Yace kuma siyasar 2027 mutane zasu bi ra’ayin ‘yan siyasa na kusa dasu ne wajan zabe.

Karanta Wannan  APC ta zargi cewa 'yan Adawa ne ke daukar nauyin harè-hàrèn da 'yan Bìndìgà ke kaiwa dan kawai ace Tinubu bai iya mulki ba baya kokari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *