
Tauraron Fina-finan Hausa da ake kira da Anfara ya bayyana cewa yayi dana sanin shiga harkar Fim.
Ya bayyana hakane a hirar da Hadiza Gabon ta yi dashi inda ta tambayeshi wane abune yayi wanda yake dana saninsa.
Yace shiga harkar fim itace a ko da yaushe idan ya tuna abin na damunsa sosai.
Yace dalilin da yasa ba zai fita daga harkar fim ba shine idan ya fita zai fara daga farko ne a rayuwarsa.