
Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, yayi mamaki da ya ji Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanashi a matsayin makiyinsa.
Yace, shi baya kallon Kwankwaso a matsayin makiyi.
Yace ya kamata ace sun wuce wannan wurin, Yace a yanzu hadin kai a Kano na da matukar Muhimmanci.
Yace yana kiran Kwankwaso ya hakura da siyasa ya sanyawa zuciyarsa ruwan sanyi.
Ganduje ya kuma yiwa Abba maraba da zuwa jam’iyyar APC.