Saturday, December 13
Shadow

Na yiwa Atiku Makarkashiya a zaben shekarar 2023 duk na ni dan PDP ne hakanan idan ya sake tsayawa takara a shekarar 2027 zan sake yi masa makarkashiya>>Inji Ayodele Fayose

Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayse ya bayyana cewa, a zaben shekarar 2023 ya yiwa Atiku Abubakar makarkashiya.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels.

Yace babbar matsalar da aka samu a PDP shine da aka baiwa dan Arewa damar tsayawa takarar shugaban kasa bayan da dan Arewa ya kammala shekaru 8 yana mulki.

Yace Najeriya tafi PDP muhimmanci.

Yace kuma idan Atiku ya sake cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, zai sake yi masa makarkashiya.

Hakan ya zowa mutane da yawa da bazata musamman ganin cewa, shi Fayose dan PDP ne.

Karanta Wannan  Kalli Yanda aka ratayawa wata Barauniya taya za'a koneta bayan kamata tana sata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *