Monday, December 16
Shadow

NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarin Sniper don taskance abinci

Hukumar Kula da Inganci da Abinci ta Najeriya, NAFDAC ta gargaɗin ‘yan ƙasar dangane da amfani da wani sinadarin adana abinci da ake kira Sniper.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa shafinta na intanet ta ce tana ankarar da jama’a game da illar amfani da sinadarin wajen kare abinci daga lalacewa.

Hukumar ta ce tun a shekarar 2019 aka haramta sayarwa da amfani da sinadarin da ke cikin ƙananan ƙwalabe.

Yayin da aka sahalewa sayar da manyan kwabale musamman ga amintattun masu samar da magungunan ƙwari ga manoma.

A baya-bayan nan ne dai wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a ƙasar ya nuna yadda wasu ke amfani da sinadarin wajen adana nau’o’in abinci, kamar kifi da wake da wasunsu.

Karanta Wannan  Kalli Hoto: An dakatar da Dan kwallo Kungiyar Monaco Mohamed Camara saboda yaki yadda yayi tallar Luwadi

Yayin da take mayar da martani kan bidiyon shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta buƙaci ‘yan kasuwa da dillalai su guji amfani da sinadarin wajen adana abincin da mutane ke ci.

Ta kuma ce amfani da magungunan na da matuƙar illa ga lafiyar mutane, inda ta ce maganin ka iya daɗewa yana illa a jikin mutane.

”Amfani da sinarin ta hanyar da ba ta dace ba ka iya zama mummunar illa da lafiyar ɗan’adam, ciki har da haifar yara masu lalurar nakasa da mantuwa da rage haihuwa da ma kamuwa da cutar kansa”, in ji sanarwar.

Hukumar ta ce sakamakon waɗannan illoli da sinadarin ke haifarwa ya zama wajibi a gareta ta fito ta yi wa jama’a bayani, domin ɗaukar matakan kariya don kauce wa jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Karanta Wannan  Hotuna: Wakilan hukumar zaben Najeriya, INEC sun ze saka ido a zaben kasar Amurka

A cikin wani makamanci wannan gargaɗi daraktar kula da magungunan dabbobi ta ƙasar, Dakta Ramatu Momodu ta ce amfani da irin wannan sinadaran musamman na magungunan ƙwari, domin taskance abinci irin su wake daga lalacewa ba hanya ce sahihiya da hukumomin lafiya suka amince da ita ba.

Datka Momodu ta ƙara da cewa akwai hanyoyi da dama da aka amince da su na amfani da magungunan kashe ƙwari, wanda ta ce kamfanonin sarrafa magungunan sun yi tanadin yadda za a yi amfani da su, don kauce wa wuce kima.

Ta ƙara da cewa to ko su ma waɗannan ba a amince a yi amfani da su kan abincin da mutane ke ci ba, sakamakon mummunan hatsarin da ke tattare da yin hakan ga lafiyar mutane.

Karanta Wannan  Idan Ka Ce Mun Karbi Milyąɲ 16 Kai Kuma Ka Karbi Tálíyą, Ka Ga Kenan Ko A Nan Malumta Ta Yi Rana, Martanin Shéikh Umar Zaria Ga Masu Zargin Gwamnati Ta Tòshewa Malamái Baki Da Kudi Kan Matsalolin Nąjeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *