
Sanata Olusola Adeyeye ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi yunkurin basu naira Naira Miliyan 70 kowannensu dan su bashi dama ya zarce akan kujerar mulki karo na 3.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV ranar Lahadi inda yace an musu matsin lamba sosai akan su yadda Obasanjo ya zarce a karo na 3 inda aka hada musu hadda kudi.
Adeyeye yace a lokacin Aminu Bello Masari ne kakakin majalisar kuma yana gode masa sosai da bashi kariya da yayi.
Yace Masari yayi kamar yana tare da shugaban kasa amma a zahiri baya tare dashi, yace bayan da aka sha zanga-zanga da matsi da tattaunawa, ‘yan majalisar sun ki amincewa da canja fasalin kundin tsarin mulki wanda zai ba tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo damar ci gaba da mulki wanda kuma da hakan ya zamarwa kasarnan matsala.