
A jiyane dai muka ga wata mata data fito take ikirarin fasto Ebuka Obi na cocin Zion Prayer Movement Outreach ya mata addu’a inda daga Dubu dari uku da take dashi har ta sayi gidan Naira Miliyan 500.
Saidai daga baya an ga matar na sayar da lemu wanda lamarin ya baiwa mutane mamaki akai ta yada hotunan ta i da aka rika zargin faston da hada baki da ita dan ya nuna addu’ar sa na aiki.
Saidai da yake martani game da lamarin, Fasto Ebuka Obi yace bai san matar ba kuma babu wani a cocinsa da ya santa inda yace har gaban Allah ta zo ta yi karya.
Yace dama a baya ya fada cewa, sunansa zai ta yawo a kafafen yada labarai nan ba da dadewa ba akan labarin karya.