Friday, December 5
Shadow

Najeriya na shirin kwaso ‘yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida.

Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar.

Wata sanarwa da Ma’iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen.

“An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui,” a cewar sanarwar.

“Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami’an tsaro a ranar Asabar.”

Karanta Wannan  Bidiyo Gwanin Ban Tausai:Kalli Yanda 'Yan Damfara suka yiwa wani Alhaji Wayau suka kwace masa dala $1000 takardun dala $100 suka bashi dala $9 takardun dala daya-daya da sunan sun masa canji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *