Friday, December 12
Shadow

Najeriya ta lalace, sai an sha wuya kamin ta dawo daidai>>Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Najeriya ta samu matsalar rashin kula a baya dan haka gyaranta sai an sha wuya.

Ya bayyana hakane ta bakin wakilinsa, Hakim Baba Ahmad a yayin da ya wakilceshi zuwa taron karfafa Dimokradiyya a Abuja jiya.

Ya kara da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana sane da irin halin matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke ciki kuma zai dauki matakin gyara a inda ya kamata.

Ya kara da cewa, Gwamnatinsu da Bola Ahmad Tinubu ke jagoranta zata ci gaba da yaki da rashawa da cin hanci da tada komadar tattalin arziki da ci gaba da goyon bayan zaben gaskiya.

Karanta Wannan  Kabir Gombe Kazami ne, Kuma kwanannan shi da Sheikh Bala Lau suka kwacewa marayu makaranta a Gombe, aikinsu kenan zalintar marayu, Sheikh Musa Salihu Alburham da Wani malamin Izalan Jos suka soki Shugabancin Izala na kasa

1 Comment

  • Sunusi Adamu Guduma

    Hardship Al’umma suna cikin kunci, talauci, yinwa, tsadan rayuwa, ga matasalan rashin tsaro a Arewacin Nigeria, muna rokon Allah ya kawo mana saukin rayuwa, sannan shuwagabanninmu muna muku Adduan Allah ya baku ikon mana Adalci wajen inganta tsaro, samar wa matasa aikinyi, inganta Asibitoci tare da samar da likitoci da magunguna, sannan inganta harkan ilimi, inganta harkan noma da kiwo, Allah ya kawo mana saukin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *