
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, An samu tsaro sosai a Najeriya a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Daniel Bwala yace kamin hawan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu mulki ana garkuwa da mutane yanda aka ga dama har cikin Abuja da rana tsaka ana garkuwa da mutane amma wannan duk ya kau.
Yace an fasa gidajen yari da dama a mulkin baya amma a zamanin Tinubu lamura sun gyaru