Friday, December 5
Shadow

Nan da shekarar 2050 yawan ‘yan Najeriya zai karu kuma matsalar tsaro da hakan zai iya haifarwa yafi wanda ake ciki yanzu>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo yayi gargadi

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, yawan ‘yan Najeriya da ake da su zai iya karuwa zuwa Miliyan 400 nan da shekarar 2050.

Obasanjo ya bayyana hakane yayin bude wani sabon gurin kimiyya da Fasaha a jihar Sokoto.

Yace nan da shekaru 25 idan ‘yan Najeriya suka karu suna bukatar aikin yi da abinci wanda idan basu samu ba, hakan zai iya kawo matsala.

Yace hanya daya ce ta magance wannan matsala itace tun yanzu a baiwa matasa masu tasowa Ilimi.

Yace idan kuwa ba haka ba, matsalar tsaron da za’a fuskanta nan gaba tafi wadda ake ciki yanzu.

Karanta Wannan  Ni Dai da in Aikata Alfasha da Me Bakin Kyss wallahi gara Inyi Khadari abuna ya guntule>>Inji Ustaz Hussaini a yayin da suke musayar kalamai tsakaninsa da me bakin Kiss

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *