Friday, December 5
Shadow

Nasarar Rayuwa bata dogara akan karatun Bòkò ba>>Inji Gwamnan Jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Dr. Bala Mohammed ya bayyana cewa, Nasarar Rayuwa bata dogara akan karantun Boko ba.

Gwamnan ya bayyana hakane a yayin ganawa da masu sana’o’in hannu a jiharsa inda yace musu su mayar da hankali kan sana’o’insu sannan su kaucewa shiga dabi’un da zasu wargaza rayuwarsu.

Yace mutane da yawa da suka yi nasara a rayuwa sun fara ne da sana’o’i kanana kuma basu dogara da karatun boko ba.

Yace karatun Boko kawai ana yi ne dai amma karatun Qur’ani shine abin yi.

Yace musamman direbobi suna zama masu kudi sosai.

Karanta Wannan  Dokar tilastawa 'yan Najeriya su rika yin zabe ba zata yi aiki ba>>Inji Femi Falana SAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *