Nasarorin Shekaru biyun Tinubu ta wuce ta mulkin Obasanjo kawo ayyukan ci gaba – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya cimma wa a shekarun sa guda biyu na mulki, ya wuce wanda PDP ta yi a ƙarƙashin Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa Daniel Bwala ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar a shafin sa na X a ranar Juma’a.
Ya ce PDP a ƙarƙashin Obasanja ta samu tagomashi daga duniya ciki har da yafe mata bashi da samun gangar mai da yawa da fata na ƙasashe bayan dawowa mulkin dimokuraɗiyya.
Daga Usman Salisu