
Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Obong Victor Attah ya bayana cewa, ya so samarwa da mutanen jiharsa Wutar Lantarki da bata daukewa amma Shugaban kasa ya hanashi.
Yace a wancan lokacin ya gina tashar samar da wutar lantarkin kuma har shugaban kasa ya je ya kaddamar da ita.
Yace amma da shugaban kasa ya koma Abuja sai yayi sabuwar doka cewa jihohi ba zasu iya samar da wuta kuma su rarrabata ba.
Yace a haka aikin ya lalace.