Sunday, September 20
Shadow

Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai

Rahotanni daga Legas na cewa, Dangote ya rage farashin Man fetur inda gidan man MRS ya fara sayar da man akan Naira 739 akan kowace lita.

An ga masu motoci na ta layin shiga gidaje man MRS a Legas dan sayen man me sauki.

Hakan na zuwane bayan da Dangote ya rage farashin da yake sayarwa gidajen man fetur zuwa Naira 699 akan kowace lita.

Dangote dai yasha Alwashin wannan ragi zai kai kowane sashi na Najeriya inda yace za’a rika sayen man aka Naira 740 akan kowace lita.

Ya zargi ‘yan kasuwar man fetur da ke shigo da man daga kasashen waje da kara masa kudi da gangan dan su ci kazamar riba.

Karanta Wannan  Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya bai wa dakarunsa wa’adin wata guda su kawar da ‘yan bìndìgà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *