
Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mayarwa da Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima martani kan sukar da ya masa.
Injiya Buba Galadima ya bayyana Ganduje a matsayin wanda bashi da wani muhimmanci a siyasance.
Saidai a martanin Ganduje yace shi kuwa ke da muhimmanci dan sau biyu a jere ya zama Gwamnan Kano.
Sannan yace ayyukan da ya gudanar suna nan har yanzu ana ganinsu.
Yace kuma APC a karkashinsa sai kara ci gaba take amma jam’iyyar su buba Galadima NNPP sai ci baya take banda rikicin cikin gida babu abinda suke fama dashi.
Yace sannan shi kanshi Buba Galadima a siyasance babu wani abu da zai nuna na ci gaba da ya samu dan ko dawwamammen jam’iyya baya da ita.