Tauraron Fina-finan Hausa, Haruna Talle Mai fata ya bayyana cewa, shi a yanzu bakin jini gareshi inda yace yanzu babu budurwar dake sonsa.
Ya bayyana hakane a hirar da abokiyar aikinsa, Hadiza Gabon ta yi dashi a shirinta na shafin Youtube.
Talle ya bayyana abubuwan da suka dauki hankali a cikin hirar tasu ciki hadda inda yake cewa yayi nadamar barin sana’ar fata ya koma harkar fim.