
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce da kansa zai jagoranci yaki da Iran idan tattaunawar da ake yi da kasar bai cimma matsaya ba na kokarin hanata mallakar makamashin kare dangi ba.
Yace ba zasu bari Iran ta mallaki makamin ba. Inda ya zargi tsohon shugaban kasar, Joe Biden da barin Iran ta samu tarin arziki.
Da aka tambayeshi ko Shugaban kasar Israela, Benjamin Netanyahu zai iya sawa ya shiga yaki da Iran ba tare da ya shirya ba?
Trump yace a’a, yace yafi son a samu matsaya maimakon yaki amma idan ba’a cimma matsaya ba zai yi yaki da Iran.