
Sanata Kabiru Marafa daga jihar Zamfara ya bayyana cewa yana goyon bayan harin da Amurka ke son kawowa Najeriya.
Sanata Marafa ya bayyana hakane a wata hira da yayi da Gidan Talabijin na Channels TV.
Ya bayyana cewa, idan babu shugaban Musulunci a Duniya da zai yi magana dan baiwa musulmai kariya to bai ga laifi ba dan Donald Trump yayi magana da baiwa Kiristoci kariya ba.
Yace kuma misali idan ta tabbata kiristoci suka samu kariya a Najeriya an san samu ci gaba.