Wednesday, January 8
Shadow

Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Najeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike gibin da take samu wajen hako mai wanda Kungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana.

Wannan shine
karon farko cikin shekaru hudu da Najeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta

Wasu alkaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara.

A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Najeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sakamakon gazawar Najeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a bangaren tattalin arzikin sakamakon raguwar kudaden shiga da masu zuba jari.

Karanta Wannan  Labari Me Dadi: Saboda karin kudin man fetur da NNPCL ta yi, Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN tace zata shigo da mai me arha daga kasashen waje

Sai dai jim kadan da darewar Shugaba Tinubu karagar mulkin kasar, ya lashi takobin dawo da Najeriya gurbinta ta hanyar magance matsalolin tsaron yankin da ke da arzikin man dama Najeriya baki daya.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya danganta wannan nasarar da kokarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na ganin an kara yawan albarkatun man fetur da suka hada da jawo jarin kasashen waje da kuma tabbatar da zaman lafiyar al’ummomin da ke zaune a yankunan haƙar mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *