
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, bai goyi bayan korar da akawa ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP ba.
Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Gyang Bere.
Hakan na zuwane bayan da PDP ta sanar da korar Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga cikin jam’iyyar.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna wannan masala a taron gwamnonin jam’iyyar ba hakanan ba’a san da ita ba dan haka shi baya goyon bayan korar Wike.