Tuesday, May 19
Shadow

Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, bai goyi bayan korar da akawa ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP ba.

Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Gyang Bere.

Hakan na zuwane bayan da PDP ta sanar da korar Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga cikin jam’iyyar.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna wannan masala a taron gwamnonin jam’iyyar ba hakanan ba’a san da ita ba dan haka shi baya goyon bayan korar Wike.

Karanta Wannan  Wata Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta je kusa da Abuja ta kafa sansani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *