Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa,shine zai lashe zaben shekarar 2027 saboda PDP ta mutu.
Ya bayyana hakane a Katsina bayan kaddamar da ofishin jam’iyyar a kan hanyar IBB Way.
Kwankwaso yayi kira ga mutanen jam’iyyarsa da kada su yadda a yaudaresu da Taliya da kudi yayin zabe inda ya jawo hankalinsu kan su ci gaba da aiki tukuru dan ci gaban jam’iyyar.