Wednesday, October 9
Shadow

Ashe Shugaba Tinubu korar me magana da yawunsa Ajuri Ngelale yayi, ji bayani dalla-dalla

Rahotanni na ta kara fitowa kan dalilin ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa,Ajuri Ngelale.

A ranar Asabar ne dai Ajuri ya ajiye aikin nasa inda ya bayyana dalilan rashin lafiyar danginsa a matsayin abinda yasa ya ajiye aikin.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa fada ne ko rashin jituwa tsakanin Ajuri da wasu na kusa da shugaban kasar yasa ya ajiye aikin.

Hakanan a wani sabon Rahoto na kafar FIJ, suma sun bayyana cewa, rashin jituwa ne tsakanin Ajuri da dayan kakakin shugaban Bayo Onanuga inda kowa kw ganin shine babba a tsakanin su.

Majiyar tace an yi yunkurij sasantasu amma Ajuri yaki yadda a yi musu sulhu wanda haka tasa daga baya aka koreshi daga aiki.

Karanta Wannan  Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa

Saidai bayan da aka koreshi daga aikin,ya yi rokon a taimaka masa yayi ritaya da kansa dan idan akace an koreshi ya zamar masa abin kunya.

Hakanan itama fadar shugaban kasar da ta lura idan aka ce korar Ajuri aka yi abin zai zamar mata abin kunya shine ta amince masa da ya ajiye aikin maimakon ace korarsa aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *