
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya kai ziyara Kontagora jihar Naija a yau inda ya gana da iyayen daliban makarantar St. Mary’s da aka yi garkuwa dasu.
Wannan na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na kawo karshen matsalar da kuma nunawa iyayen daliban damuwa da halin da suke ciki.