
Shugaban marasa Rinjaye na majalisar Dattijai Abba Moro ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da ya koma APC ne silar faduwar PDP zaben shugaban kasa a 2023.
Yace Okowa ko jiharsa bai ci ba, inda yace da wani aka dauko daga kudu ba Okowa ba da za’a iya samun Nasara.
Ya fadi wannan maganane a matsayin ga Ifeanyi Okowa da yace yayi dana sanin yin takarar neman shugabancin kasa da Atiku.
Moro yace Ifeanyi Okowa idi rufe ya je PDP yana neman a bashi takarar mataimakin shugaban kasa inda yace babu wanda ya tursasashi.