Mahajjaci dan Najeriya ya rasu a kasar Saudiyya
Rahotanni sun bayyana cewa, mahajjaci dan Najeriya daga jihar Legas ya rasu a kasar Saudiyya.
Idris Oloshogbo dan shekaru 68 ya rasu ne bayan ya kammala dawafi yana cikin cin abinci.
Jami'an lafiya na kasar Saudiyya sun tabbatar da rasuwar Idris.
Sakataren hukumar kula da walwalar Alhazai ta jihar Legas, Saheed Onipede ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna mika ta'aziyya ga iyalan mamacin.