Banbancin maniyyi da maziyyi
Maniyyi da maziyyi suna da bambance-bambance masu muhimmanci, musamman dangane da sifa da kuma yadda ake kula da su a cikin addinin Musulunci:
Maniyyi:
Asali: Maniyyi shine ruwan sha'awa wanda yake fitowa yayin inzali (orgasm). Yana fitowa ne da karfi daya bayan daya, zaka jishi tsul-tsul kuma ana jin dadi sosai yayin fitarsa.
Sifa: Yana da kauri, launin fari, yana kuma da yauki, idan ya bushe yana zama kamar koko, waja zai yi fari.
Hukunci: Maniyyi ana daukarsa da tsarki a mafi yawan mazhabobi ba najasa bane,idan ya taba kaya za'a iya yin sallah dasu ko da ba'a wanke ba, kankarewa ta wadatar. Amma idan ya fita, ana bukatar yin wanka (ghusl).
MaziYYi:
Asali: MaziYYi shine ruwan sha'awa wanda yake fitowa yayin tunanin saduwa ko sha'awa, kafin inzali. Yawanci zaka ga ya ...

