PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu
Jam’iyyar PDP ta bayyana ranar Alhamis 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa karo na biyu a shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa, a taron farko da hukumar NEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu,an tattauna batutuwan da suka hada da makomar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Illiya Damagum, an daga shi zuwa taron NEC na gaba wanda aka shirya tun watan Agusta.
Kungiyar ‘yan jam’iyyar ta Arewa ta tsakiya ta ce za a zabi dan takara daga shiyyar don kammala wa’adin tsohon shugaban Jam’iyyar na kasa, Dr. Iyiorchia Ayu, wanda ya yi murabus kusan shekaru biyu cikin wa’adinsa na shekaru hudu.
Gabanin taron NEC na watan Satumba, jam’iyyar ta tsayar da ranar 27 ga watan Yuli domin gudanar da zabubbukan mazabu/wakilai domin zaben shugabannin unguwanni da wakilai uku na wucin gadi a jihohi 23 daga cikin 36 na kasar ciki har da Abuja.
Wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa sun hada da: Akwa Ibom, Cross River, Benue, Bauchi, FCT, Taraba da Ebonyi da dai sauransu.
Wannan yana kunshe ne a cikin tsarin 2024 na jam’iyyar da aka daidaita da jadawalin ayyuka na Majalisar da aka fitar ranar Litinin.
Bisa ga jadawalin lokaci, za a yi la’akari da ƙararrakin da suka taso daga majalisun gundumomi a ranar 2 ga watan Agustan 2024.
A ranar 10 ga watan Agusta ne za a gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da na kasa kana kuma da na jihohi 21 da abin ya shafa.
Za a gabatar da kararrakin da suka taso daga majalissar Kananan Hukumomi a ranar 16 ga watan Agusta.
A ranar 31 ga watan Agusta ne za a gudanar da taruka na Jihohi a Jihohi 18. Jihohin sun hada da: Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Kano, Rivers, FCT, Benue, Katsina, Ekiti da Ebonyi da dai sauransu.
Za a yi la’akari da ƙararrakin da suka taso daga waɗannan majalisun jihohi a ranar 5 ga watan Satumba, 2024.
Daga: Abbas Yakubu Yaura