Peter Obi na da masaniya kan ziyarar da na kai wa Abure – Datti

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya ce jagoran jam’iyyar, Peter Obi, na da masaniya kan matakin da ya ɗauka na halartar taron ɓarin jam’iyyar da ke ƙarƙashin shugabancin Julius Abure.
Datti ya ce ya ɗauki matakin ne a wani yunƙuri na sulhunta ƴaƴan jam’iyyar da suka fusata.
Datti ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, bayan ziyarar tasa ta janyo ce-ce-ku-ce.
“Jam’iyyar Labour ba jam’iyya ba ce da za a yi watsi da ita, ko a gudu daga cikinta, ko a yi watsi da muhimmancinta ba,” in ji Datti.
“Ina tabbatar muku cewa kowanne mataki da nake ɗauka, ɗaukacin masu ruwa da tsaki (na jam’iyyar) na da masaniya a kai. Ba sai na shiga yin bayani dalla-dalla kan yadda muke gudanar da harkokinmu ba.”
Datti ya ce ya je taron ne don haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar da kuma neman kawo sulhu.
Jam’iyyar LP ta shafe tsawon lokaci tana fama da rikicin cikin gida, lamarin da ya sanya aka samu ɓari biyu a jam’iyyar, inda kowanne ke ikirarin kasancewa halastacce.
Ɓarin da ke ƙarƙashin jagorancin Abure, a baya-bayan nan ya bai wa Obi wa’adin ficewa daga jam’iyyar sanadiyyar rawar da yake takawa a hadakar da ƴan hamayya ke ƙoƙarin samarwa.
Peter Obi ya fi karkata ɓagaren shugabancin Nenadi Usman, wadda aka zaɓa bayan iƙirarin cewa wa’adin shugabancin Julius Abure ya ƙare