Tuesday, November 18
Shadow

Bidiyo: Ba haka ake aiki ba, wannan zubar da mutunci ne>>Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi Allah wadai da yanda wasu ‘yansanda suka yiwa wata jarumar fina-finan kudu da ta yi shigar banza rakiya

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta nuna rashin jin dadinta game da abinda wasu jami’anta suka aikata na yiwa jarumar fina-finan kudu, Angela Okorie rakiya yayin da take sanye da shigar banza take gudu.

Bidiyon nata ya watsu sosai a kafafen sada sumunta wanda hakan ya jawo cece-kuce.

Dan haka hukumar ‘yansandan ta fitar da sanarwar cewa abinda ‘yansandan suka aikata baya cikin tsarin aikin dansanda.

Hukumar tace tana kan Bincike kuma zata dauki matakin da ya dace bayan kammala binciken lamarin.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin sunayen Manya-Manyan 'yan Adawar da suka hadu a waja taron jam'iyyar ADC ta su Atiku a jiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *