Saturday, December 13
Shadow

Peter Obi ya amince ya zama mataimakin Atiku a takarar 2027 da sharadin cewa idan sun ci zabe Atiku zango daya zai yi ya sauka

Rahotanni da hutudole ke samu na cewa, Peter Obi wanda dan takarar shugaban kasa ne a shekarar 2023 ya mince ya zama mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027.

Rahotan wanda kafar jaridar Punchng ta ruwaito yace an yi zaman tattaunawa tsakanin Atiku da Peter Obi a kasar Ingila wanda a canne aka cimma wannan matsaya.

Da farko dai Atiku ya gayawa Peter Obi cewa ya zama mataimakinsa shi kuma zai yi zango data ne kawai ya sauka, Peter Obi yace a bashi lokaci zai je yayi Shawara.

Saidai Rahotan yace Tuni Peter Obi ya amince da wannan tayi.

A shekarar 2019 dai Peter Obi da Atiku sun yi takara tare amma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kayar dasu.

Karanta Wannan  A yau ne ake sa ran kasar Amurka zata fitar da bayanai na zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da safarar miyagun Kwàyòyì, Saidai fadar shugaban kasa da APC sun ce wannan ba wani abu bane, Duk abinda ya faru kamin Tinubu ya zama shugaban kasa ba'a sakashi a lissafi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *