
Ba Daidai Ba Ne Raba Motocin Kamfen Yayin Da Talakawa Ke Fama Da Yunwa, Obi Ya Soki Gwamnatin Tinubu
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya soki raba motocin alfarma ga wakilan ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors domin shirye-shiryen zaɓen 2027, lamarin da ya danganta ga gwamnatin Tinubu.
A sanarwar da ya fitar, Obi ya ce wannan aiki tsananin rashin tausayi ne da cin amana, musamman a lokacin da ƴan ƙasa ke fama da yunwa, rashin aikin yi da matsalolin tsaro.
Ya jaddada cewa maimakon kashe kuɗaɗen jama’a kan motocin kamfen, gwamnati ta mayar da hankali kan samar da abinci, kiwon lafiya, ayyukan yi da inganta tsaro.