
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta lashe kofin Championships League bayan lallasa Kungiyar Inter Milan da ci 5-0 a wasan da suka buga da yammacin yau.
Mayulu, Kvaratskhelia,Doue, da Hakimi ne suka ci mata kwallayen.
Sun kafa tarihin zama kungiya ta farko data taba lashe kofin da ci 5-0.

Dan wasan Kungiyar, Désiré Doué ya zama na farko da ya zama taimaka aka ci kwallo sannan ya ci kwallaye 2 a wasan karshe na gasar Championships League.
Wani abu da ya kara daukar hankula a wasan shine yanda magoya bayan PSG suka rika data rubutu me dauke da neman a dainawa mutanen Gàzà kisan Kare dangi.