
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta kaddamar da bikin baje-kolin fina-finan Arewacin Najeriya.
Bikin dai na son laluɓo hanyoyin fito da ƙwarewar al’ummar arewacin Najeriya.
An samu halartar ministar raya al’adun Najeriya, Hannatu Musawa da shugaban hukumar fina-finai, Ali Nuhu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.