Rahotanni sun nuna yanda Israela ta kai wani mummunan hari a wajan sansanin ‘yan gudun Hijira dake Rafah.
Harin yayi sanadiyyar wuta ta tashi a sansanin inda mutane akalla 50 suka kone kurmus.
An ta ganin gawarwakin mutane sun kone ana zakulosu a bidiyon da suke ta yawo a shafukan sada zumunta.
Saidai hakan na zuwane bayan da kotun majalisar dinkin Duniya ta baiwa Israelan umarnin daina kai hari Rafah:
Abin jira a gani shine wane mataki majalisar dinkin Duniyar zata dauka tunda dai gashi Israela bata daina kai hare-haren ba?
[…] Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin ‘yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana. […]