Friday, December 5
Shadow

Rahoto: Gwamnati ta gano gurɓacewar iska a wasu unguwanni a jihar Kano

Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da gwamnatin Kano ke saki ya nuna cewa akwai gurɓatar iska a wasu unguwanni a cikin ƙwaryar Kano, inda hakan zai ƙara ta’azzara yaɗuwar cutuka a cikin al’umma.

Rahoton, wanda Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta fitar bayan gwajin lafiyar iska da ta yi tsakanin 26 zuwa 30 ga watan Mayun da mu ka yi bankwana da shi, ya nuna cewa unguwanni kamar su Gaida, Ja’en, Sabon Titi da Sharada Kasuwa, basu da lafiyayyar iska, inda sakamakon ya nuna akwai gurɓatar iska a waɗannan unguwanni.

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Kano na shirin kai ɗauki a wadannan unguwanni sakamakon gurɓacewar iska, inda ta nuna damuwa kan karin gurɓacewar yanayi da ake samu a jihar.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbin ofisoshin 'yansanda masu kayan aiki sosai

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M Hashim ne ya wallafa rahoton a shafin sa na Facebook.

Ya kuma nuna cewa kula da muhalli hakki ne na gaba daya al’umma ba wai gwamnati kaɗai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *