
An rufe Heathrow da ke yammacin London – tashar jirgin sama mafi cunkuso a nahiyar Turai – sakamakon gobara da aka samu a kusa da cibiyar lantarki da ke kusa da filin jirgin saman.
Filin jirgin zai kasance a rufe har zuwa 12:00 na dare a yau Juma’a saboda matsalar lantarkin.
Wakilin BBC ya ce babu wata sanarwa kan lokacin da za a iya dawo da lantarkin a Heathrow kuma filin jirgin ba shi da wani zaɓi illa daukar matakin rufewa domin kare lafiyar fasinjoji da ma’aikatansa.
A bara fasinja miliyan 83 ne suka bi ta filin jirgin saman na Heathrow.