Tauraron dan kwallon MLS kuma tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa, Kungiyar Real Madrid ta fi kowace kungiya Kyau a Duniya.
Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi da wata kafa me suna Infobae.
Ya bayyana cewa idan sakamako me kyau ake magana, Real Madrid ce kungiyar data fi kowace amma idan kuma iya wasane, ya fi son Guardiola inda yace duk kungiyar da Guardiola ya horas zaka ganda ta yi fice.
Yace dan haka iya wasa sai Manchester City amma kuma sakamako sai Real Madrid.
Kuma wannan ra’ayi na Messi bai zo da mamaki ba ganin cewa, Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai.