
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya caccaki ‘yan uwansa ‘yan kudu da suke zagin jihar Bauchi saboda ta bayar da hutun Azumin watan Ramadana ga makarantu.
Omokri ya bayyana cewa fiye da sau 10 yana ziyarar jihar Bauchi.
Yace yana son jihar Bauchi kuma mutanenta wayayyu ne wanda sun san abinda suke so a rayuwa.
Sannan yace mutanen Bauchi sun zabi gwamnansu kuma suna goyon bayansa a kan duk wani abu da yayi.
Yace kuma a Dimokradiyya ake kuma mutanen Bauchi suna goyon bayan abinda gwamnatinsu ta yi na bayar da hutun watan Ramadana, dan haka bai kamata wani ya zauna a Legas, ko Fatakwal ko Anambra ya rika jin haushin wannan mataki ba.
Yace jihar Bauchi ba cima zaune bace a Najeriya, jihace wadda take bayar da gudummawa sosai wajan ci gaban Najeriya musamman ta bangaren abinci.
Yace a wasu jihohin duk ranar Litinin sai an rufe makarantu wanda idan aka lissafa kwanaki 54 kenan a shekara ko ace sati 8 kenan.
Yace irin wadannan jihohi ya kamata ace na caccaka ba Jihar Bauchi ba.