
Rahotanni sun bayyana cewa, Rikicin Jam’iyyar APC ya kara ci gaba da kazancewa inda ake cacar baki tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da sakataren jam’iyyar APC din, Ajibola Basiru.
Ajibola Basiru ya bayyana cewa, kamata yayi Wike ya sauka daga mukamin nasa saboda munanan kalaman da yayi akan jam’iyyar APC.
Wike a wajan taron da yayi a jihar Rivers yace duk wanda ke son yi musu katsalandan a siyasar jiharsu ta Rivers, zai kwashi kashinsa a hannu.
iHakan na zuwane dai yayin da rikici tsakanin Gwamnan Rivers, Simi Fubara da Wike din ke kara kazanta.
Wike ya dage cewa, Fubara ba zai tsaya takara ba a karo na biyu.