Tuesday, February 24
Shadow

Robert Prevost ne sabon fafaroma

Fadar Vatican ta sanar da cewa Robert Prevost ne sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.

Shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.

Zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).

Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

A watan Satumban 2023 ana naɗa shi a muƙamin babban limamin Cocin Katolika wato ”Cardinal’.

Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra’ayin.

Za mu ci gaba da sabnta wannan labari…

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon wani matashi daga jihar Katsina na fadin cewa, bai taba samun farin ciki irin na gwamnatin Tinubu ba, Yace da mata daya gareshi yanzu ya kara, hakanan kasuwarsa ta habaka kuma matsalar 'yan Bìndìgà ta gushe a karamar hukumarsa ta Jibia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *