Sunday, January 5
Shadow

Rundunar ‘yansanda a Katsina ta ce ta kashe ‘yanfashi 40 a 2024

Kwamashinan ‘yansanda na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aliyu Musa, ya ce rundunarsu ta kashe ‘yanfashin daji 40 daga farko zuwa ƙarshen shekarar 2024.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai na ƙarshen shekara a birnin Katsina ranar Litinin, kwamashinan ya ce sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 319, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kazalika a cewarsa, sun kama aƙalla mutum 916 a wannan tsakanin.

“Mun samu nasarar ɗaiɗaita gungun miyagu da dama, mun ƙwato makamai, mun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mun yi nasarar gurfanar da wasu da dama a gaban kotu,” in ji shi.

Karanta Wannan  AL'AJABI: Bunsuru Ya Raka Gàwaŕ Wata Ďàttìjuwa Zuwa Makabarta A Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *