
Matatar man fetur ta Dangote tace sabbin motocin jigilar man fetur data kawo guda 4000 zasu samar da ayyukan yi na kai tsaye guda 15,000.
Matatar tace mutanen da zasu samu ayyukan sun hada da Direbobi da manajoji da sauransu.
Matatar man fetur din tace ta kashe Naira Biliyan 720 wajan sayo wadannan motocin jigilar man fetur din.
Matatar tace zata kashw naira Tiriliyan N1.07 waja rabon man fetur din a shekara.
Tace nan da 15 ga watan Augusta zata fara raba man zuwa gidajen man fetur da manyan masana’antu da sauran manyan masu amfani da man fetur a fadin Najeriya.
Matatar tace wannan tsari zai amfani kananan masana’antu guda miliyan 42.