
Wasu Rahotanni daga bangaren masu goyon bayan Najeriya sun bayyana cewa jirgin saman C-130 da ke kasar Burkina Faso ba tursasa masa aka yi ya sauka ba.
Jirgin ya sauka ne saboda samun Tangarda a yayin da yake kan hanya.
Saidai hakan na zuwane bayan da ita kasar Burkina Faso tace jirgin ya shigar mata kasa ne ba bisa ka’ida ba.
Zuwa yanzu dau hukumar sojojin saman Najeriya basu fitar da sanarwa ba game da lamarin.