
A baya mun samu rahoto daga Sahara reporters cewa an kama wasu sojoji 16 da suka yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.
Duk da hukumar sojoji tace sojojin sun aikata wasu laifuka ne na rashin da’a, Saidai Sahara reporters tace juyin Mulki ne sojojin suka shirya amma ake boye maganar.
Hakanan kafar Premium times itama ta tabbatar da cewa aojojin sun shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin mulki ne.
Hakanan an kamasu ne tun kamin ranar 1 ga watan October, sannan su kusan 20 ne a cewar Sahara reporters
Hakanan premium times tace sojojin sun shirya yin juyin mulkinne ranar 25 ga watan October inda suka so kashe ahugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio, dana wakilai, Tajudeen Abbas.
Sannan sun so kama manyan hafsoshin tsaro na kasarnan.
Sun kuma yi aiki ne tare da wasu dake taimaka musu da bayanai daga fadar shugaban kasa.
Saidai Premium times tace tuni aka kama sojojin aka kuma kafa kwamitin da zai bincikesu.